Da’awah Da Lacca Ba Zai Rike Ka Da Iyalin Ka Ba, Ka Tafi Ka Nemo Babban Aiki – Abdullahi Ishaq

Biyo bayan cece kuce dayake ta faruwa tsakanin Abdullahi Ishaq Jibrin masanin bincike da leken asiri da tsohon maigidan shi wato Rtd AIG Ahmad AbdurRahman inda a lokutta mabambamta Abdullahi Ishaq ya zargi maigidan na shi akan ya dauke shi aiki Babban mataimaki wato PA zuwa Gidan gwamnatin Bauchi amma daga baya sai AIG AbdurRahman idon shi ya rufe, ya wulakanta da cin mutuncin shi har yayi mishi sharrin ana zargin shi Abdullahin PA da bincikan Gwamna Bala Muhammad na Bauchi inda yayi amfani da wannan dama ya jefar da Abdullahi, alhali kuwa ashe yayi haka ne don son zuciyan shi ne da mugunta. Har zuwa wannan lokacin bai biya Abdullahi kudin aikin watannin hudu da yayi mishi ba a matsayi PA ba.

Tun daga wannan lokacin dangantakan shi da maigidan na shi tayi tsami. Cikin wata tattaunawa da Abdullahi Ishaq yayi da wakilin mu, ya shaida wa jaridan mu cewa tsohon maigidan na shi yayi murabus kaman yanda shima ya karanta a wata jaridan yanar gizo na jihar Bauchi mai suna Zamani TV a jiya Juma’a 12th September 2025 to amma babu wani hakikannin kwanan wata daya nuna ranan da yayi murabus din, inji Abdullahi.

Bisa abin da da ita jaridan ta rawaito, AIG AbdurRahman dai yace yayi murabus ne akan raayin kan shi ne don ya kara kullawa da Iyalin shi da kuma fuskantan Da’awah da kuma bada Lacca. Biyo bayan wannan bayanin na AIG Ahmad AbdurRahman shine Abdullahi ya kalubalance shi akan cewa akwai rainin hankali a cikin jawabin don ai shekara guda daidai kenan da bashi wannan mukamin na mai ba Gwamnan Bauchi shawara akan harkan tsaro to amma duk dayake shi mai son kulawa da Iyalin shi ne mai yasa tun farko ya nemi mukamin, sannan kuma ai ko da yake rike da mukamin babu abinda ya tsinana sai dai tafiye tafiye da sunan Da’awah a garuruwa dabam dabam. Toh meyasa zai fada wa duniya cewa saboda wadannan dalilan ne yayi murabus, ko kuwa sai yanzun ne ya san mihimmmancin iyalin shi.

Koma dai menene dalilin murabus din shi gaskiya zata bayyana ko mu dade ko mu jima In sha Allah. Babban shawara ga AIG AbdurRahman shine komin girman gona akwai kuyyan karshe kuma duk abinda yayi farko tabbas zai yi karshe. Ya tafi dani Bauchi yaci mutunci na kuma gashi cikin yardan Allah, ya dawo Kaduna ya same ni. A karshe ina taya shi murnan ajiye aiki da yayi kuma ina kara bashi shawara a shirye nake in taya shi rarraba takardun neman wani aikin wato CV saboda dogaro da Da’awah da Lacca ba zai iya daukan nauyin Iyalin shi ba.


Leave a comment



Design a site like this with WordPress.com
Get started