
SANARWA!
Offishin Shugaban Hukumar Ilimin Amajirai da Yaran da Basa Zuwa Makaranta, Dr. Muhammad Sani Idris na sanar da daukacin ‘yan uwanmu almajirai na tsangayu cewa acikin tsare-tsarenta na inganta al’amuran tsangayu da kuma kyautatata rayuwar almajirai, na sanar da daukacin gwanaye da alarammomi da malamai masu tsangayoyi cewa ta shirya gudanar da wani kwas na almajiran tsangaya wanda za a yi a Jihar Kaduna. Wannan kwas din za a yi shi ne na tsawon. wata tara. Saboda haka, kowanne almajiri, dan tsangaya wanda ya cika sharudan da Za ayyana, kuma yake da sha’awar shiga wannan kwas din sai ya rubuta sunansa da tsangayarsa da sunan alarammansa da kuma garinsa, ya tura ta shafinmu na facebook ko kuma ya kirawo Sadiq ko kuma ya tura masa whatsapp ta wannan lambar 09064313510 yace ina sha’awar kwas din kuma na cika sharuda.
Sharudan su ne kamar haka:
- Dole ne mai sha’awar wannan kwas din yazama dalibin makarantar tsangaya.
2- Dole ya zama mahaddacin Alkur’ani
3- Kada shekarunsa su kasa shekara goma sha shida ko su zarce ashirin da shida
4- Ya zama yana da cikakken lafiya da za a iya bashi horo daga karfe takwas na safe zuwa shida na yamma
5- Ya zama ya samu amincewar malaminsa na tsangaya da kuma iyayensa
6- Yazama bashi da wata matsala da jami’an tsaro ko wata kotun kasa.
Wannan course din zai mayar da hankali wajen ilimintar da almajirai da kuma koya musu sana’o’i wadanda za su basu damar bayan gama kwas din, su zama zasu iya rike kansu batare da sun dogara da kowa ba wajen harkar neman abinci da rayuwa.
Guraben karatun nan basu da yawa.
Saboda haka, duk wanda ya rubuta sunansa da lambarsa kafin Alhamis mai zuwa, 30 ga watan Janairu, 2025, daidai da 30 ga watan Rajab, 1446 .
Hukumar gudanarwa za ta tuntube shi domin fada masa mataki na gaba.
Muna fata za a fara wannnan kwas din kafin 15 ga watan Fabarairu, 2025. Allah Ya sa wannan abu da za mu yi ya zame mana mai amfani duniya da qiyama.
MB: Dangane da yaran da basa zuwa makaranta na arewaci da kudancin Nigeria,su kuma za su samu tasu sanarwar nan da makonni biyu.
Signed.
Dr. Muhammad Sani Idris
Executive Secretary.