
Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsanma, a jihar katsina, wato Federal University Dutsanma, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya baiyana cewa a matsayin su na shugabanni na jami’oi basu goyon bayan Zanga-zanga da ake shirin yi a fadin kasar najeriya.
Farfesa Bichi ya baiyana hakanne a zantawar sa da manema labarai.
Shugaban Jami’ar ta Dutsanma FUDMA, ya kawo misalai da yawa da yasa baza su goyi bayan Zanga-zanga ba.
“Misali, zanga-zangar da ta kifar da Gwamnatin kasar Sudan Saboda kawai an Kara farashin kudin burodi a kasar, sudan tana cikin mawuyacin hali fiye da kafin zanga-zangar, Wanda kafin wannan halin kasar wata farfajiya che ta ilmi Wanda har ‘Yan Najeriya suna zuwa Sudan karatu, amma yanzu karatu ya gagara, Saboda Babu zaman lafiya a kasar.
“Haka zalika, idan aka Fara zanga-zanga mafi yawan abubuwan da ke faruwa Kamar yanda ya faru a wasu kasashe, irin su SUDAN, LIBIYA, RUWANDA, KENYA, da sauransu, lamarin yakan rikide ya koma ta’addanci, domin za’a rika lakata duk wani abu muhimmi a kasa, za’a koma kashe-kashe da kone-kone, za’a rika fasa manyan kantuna da shaguna ana sacewa da kwashe dukiyar al’umma, zai koma rikicin kabilanci da adding, wannan fa shi ne zanga zangar da ake kokarin yi, daga karshe za’a hambarar da Gwamnati, Wanda wannan zai ba Yan ta’addan da ke daji damar shigowa su kafa Gwamnati da doka yanda suke so Kamar yanda ya faru a wasu kasashe”.
” Za mu shiga halin ha’u lai, mu gwammace da a ayi zanga-zanga ba, domin matsalar da za a fuskantasai yafi Wanda muke ciki a yanzu”.
Farfesa Bichi yayi kira ga matasa da dalibai da suke karatu a sassa daban-daban na kasarnan da kar su yarda ayi amfani dasu wurin yin zanga-zanga da bazan tayi tasiri ba.
Yayi kuma kira da rokon shuwagabanni a najeriya da su duba hali da yanayi da al’umma ke ciki na kunci, talauci da tsadar rayuwa domin a samu mafita.