
Hukumomin jami’ar tarayya da ke Dutsin Ma a jihar Katsina, sun tabbatar da kubutar da daliban da ‘yan bindiga suka sace watanni uku da suka gabata.
Shugaban jami’ar Professor Armaya’u Hamisu Bichi ne ya tabbatar wa DW kubutar da daliban, inda ya ce yanzu haka suna kan hanyar zuwa Abuja, ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, inda za a duba lafiyarsu.
Daga bisani kuma za a hada su da iyayensu.