2023: Uba Sani zai zama shugaba nagari, in ji Kwamared Musa Mohammed

‘Sanata Uba Sani a wurina, zai zama shugaba nagari. Na yi imani da haka. Na yi hulda da shi’

Shugaba ne nagari Wanda muke da yakinin zai gina tsarin mulkinsa akan dokokin kasa da tabbatar da hukunta duk wanda ya take doka. 

Uba Sani shugaba ne mai baiwa da hangen nesa yanda zai ci da al’ummarsa gaba.

Uba Sani shugaban da yake girmama matsayin sauran ma’aikata dake aiki a karkashinsa, shugaba ne nagari. Hakan na nufin zai iya baiwa kowa hakkin aikinsa da daraja daidai da yanda karfin doka ta ba shi.

Uba Sani dan siyasa ne, mutumin kirki ne ɗan ƙwarai, mai amana, ko kaɗan ba shi da girman kai. Gwarzon shugaba ne managarci wanda ba shi da kasala, yana tafiyar da al’amuransa lillahi, babu nuƙu-nuƙu ba almundahana, mai haƙuri da juriya, uwa uba kuma mai riƙo da addini ne.

Kaduna za ta kara martabarta a idon duniya, na zaman ta jiha mafi bunƙasar kasuwanci da zaman lafiya, tarbiyya, gami da al’amuran yau da kullum.

Saboda haka wanann Dan takarar Gwamna a jihar kaduna Kuma jagoran talakawan jihar ‘SANATA UBA SANI’ mai aƙida irin Na Margayi Sardauna Wanda shine zai ɗora jihar a bisa tsarin da ya kamaceta.

Kungiyar Rundunar nasara, mutane ne masu goyon bayan takarar kujerar Gwamna da Uba Sani keyi, kuma masu manufa da tsari da burin ɗora jihar Kaduna a mizanin jihar da za ta yiwa sauran jihohi fintinkau wajen tattalin arziƙi, noma kiwo da bunƙasa ƙananan sana’oi.


Leave a comment



Design a site like this with WordPress.com
Get started